Jagoran APC Bola Ahmed Tinubu, ya ce duk wani zababben dan majalisar tarayya na APC, tilas ya bi abin da duk jam’iyyar ta gindaya, ko kuma su sa kafar wando guda.

Tinubu, ya ce abin da jam’iyyar APC ta gindaya shi za a bi wajen warware matsalar shugabancin majalisa.

Ya dai furta haka ne bayan gudanar da addu’o’i da malamai da fastoci suka yi masa, a Legas, domin taya shi murnar cika shekaru 67 a duniya.

Ya ce yi wa jam’iyya da’a shi ne babban ginshikin jam’iyya, domin an yi sakaci a 2015, da aka bada kofa har wani ya shiga cikin jam’iyyar ya hana Najeriya ci gaban da jam’iyyar ta yi alwashin samar wa.

Ya ce an dai ga yadda aka karke, don haka a wannan karo ba za a bari irin haka ta sake faruwa ba.  

Ya ce a wannan karon ko dai a zauna tare da su abi jam’iyya sau da kafa, ko kuma a fice ka bar musu jam’iyya.

Leave a Reply