Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tabbatar wa kungiyar kiristoci ta Najeriya CAN cewa zai inganta Najeriya fiye da lokacin da ya same ta a 2015.
Buhari, ya yi wannan tabbaci ne a lokacin da kungiyar ta ziyarce shi a fadar sa, karkashin jagorancin Shugaban kungiyar ta CAN, Samson Ayokunle.
Ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da kawo gyara kan muhimman kalubalen da suka addabi Najeriya, ciki kuwa har da matsalar tsaro, ta tattalin arziki da kuma cin hanci da rashawa.
Kafin nan sai da shugabannin na CAN suka shaida wa manema labarai na Fadar Shugaban Kasa cewa sun je ne domin su taya Buhari, murnar sake lashe zabe karo na biyu da ya yi.
Cikin wani jawabi da mai taimakawa shugaban kasa, kan harkokin yada labarai Femi Adesina, ya fitar, Buhari ya shaida wa maziyartan cewa sakamakon zaben da aka gudanar na shugaban kasa ya nuna yadda dimbin ‘yan Najeriya su ka yi amanna da shugabancin sa.
Ya ce zai ci gaba da tabbatar da dorewar zaman lafiya, da lumana, da kyakkyawar zamantakewa a tsakanin mabiya addinai a Najeriya.
Ya cigaba da cewa a bangaren raba mukamai kuwa, zai duba cancanta da kuma maida hankali a kan kowane yanki, ta yadda kowane yanki zai san cewa ana tafiya tare da shi.
Buhari, ya ce gwamnatin sa na kara kaimi wajen yaki kungiyar Boko Haram, tare da kara himma wajen ganin an kubutar da dukkan wadanda ke tsare a hannun su.



































