Wani jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai Farouk Adamu Aliyu, ya bayyana cewa jam’iyyar su ta APC ta koyi darasi dangane da yadda aka gudanar da zabubbukan 2019.

A wata hirara da ya yi, ya bayyana cewa dauki dora ko kuma kakaba ‘yan takara na daya daga cikin abubuwan da suka kawo ma jam’iyyar tasgaro, ya zama cewa ta fuskanci matsaloli a wasu jihohi wanda hakan ya yi sanadiyar rasa wasu kujerun gwamnoni da ma na ‘yan majalisa.

Ya bada misali da jihar Ogun inda ya bayyana cewa gwamnan ya yi Angulu da kan zabo inda gwamnan jihar dan APC ne amma ya jagoranci wata jam’iyya domin ganin cewa an kada jam’iyyar APC a zaben gwamna.

Ya kuma ba da misali da jihohin Imo da Bauchi da kuma Adamawa inda ya ce rikice-rikicen cikin gida ne suka yi sanadiyar faduwar jam’iyyar zabe a jihohin.

Ya yi kira ga jam’iyyar APC cewa a shekarar 2023 ta tabbatar an yi zaben fitar da gwani na jam’iyyar sahihi kuma ingantacce a duk fadin kasar.

Leave a Reply