Shugabannin jam’iyyar APC, za su yanke hukunci a kan yadda za a raba mukaman majalisun dokoki na tarayya a mako mai zuwa.

Biyo bayan zaben Shugaban kasa da na ‘yan majalisun dokoki na tarayya, jam’iyyar APC ta samu mafi rinjayen kujeru a majalisun biyu, lamarin da ya sa ake sa ran ita za ta kafa shugabanci.

Manyan mukamai hudu da za a yi rabo tsakanin yankuna sun hada da Shugaban majalisar dattawa, da shugaba majalisar wakilai, da mataimakin Shugaban majalisar dattawa da kuma mataimakin shugaban majalisar wakilai.

Tuni dai wasu zababbun sanatoci da ‘yan majalisar wakilai su ka nuna ra’ayin su na neman mukamai, yayin da wasu ke cewa za su amince da duk hukuncin da majalisar ta yanke.

 Daga cikin masu neman kujerar Shugaban majalisar dattawa kuwa akwai Sanata Ahmad Lawan daga jihar Yobe, da Sanata Ali Ndume daga jihar Borno, da Sanata Danjuma Goje daga jihar Gombe da Sanata Abdullahi Adamu daga jihar Nasarawa.