Shugaban hadadiyar Kungiyar kwadago ta Nijeriya ULC, ya ce ba za su amince da kari a kan harajin kayayakin masarufi da gwamnatin tarayya ke kokarin yi domin biyan sabon mafi karancin albashi ba.
Mr Ajaero ya bayyana wa manema labarai haka ne a Lagos, yayin da yak e maida wa gwamnatin tarayya martini, dangane da zancen da ta yi na neman izinin kara harajin kayan masarufi, domin samun kudin biyan sabon mafi karancin albashi na Naira 30,000.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Talata ne Majalisar Tarayya ta amince da Naira 30,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikata.
Ministan Kasafi da Tsare-tsare Sanata Udoma Udo Udoma, ya ce akwai yiwuwar gwamnati ta kara harajin kayayakin masarufi, da kashi 50 cikin 100 kafin karshen shekara ta 2019, domin ta samu damar biyan sabon albashin.
Shugaban kungiyar kwadagon ya cigaba da cewa, babu wata yarjejeniyar cewa za a kara haraji bayan an yi karin albashi a lokacin da su ka yi zaman tattaunawa game da karin albashin.