Sayen Kuri’u: Efcc Ta Kama Wani Kansila Da Shugaban Karamar Hukuma A Gombe

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta kasa rashen jihar Gombe ta kama shugaban karamar hukumar Dukku tare da kansilolin yakin bisa laifin sayen kuri’u a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.

Mai Magana da yawun hukumar zabe na jihar Mallam Bello Bajoga ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Gombe.

Bajoga ya ce ganin irin abubuwa da suka faru a baya, hukumar ta bukaci duk wanda ya samu labaran nda ake siyen kuri’a ko dillancin su ko kuma bada toshiyar baki ya kawo mata tsegumi domin daukar matakin da ya dace.

Ya kara da cewa, ana cikin gudanar da ke zabe ne aka kira jami’an hukumar EFCC aka shaida masu cewa, wasu na siyan kuri’u, wanda hakan ya sa jami’an ba su yi kasa a gwiwa ba wajen isa inda ake aikata wannan haramtaccen kasuwanci.

Mallam Bello ya ce tuni sun kama kasilan da ake zargin da bada kudi kana sun gayyaci shugaban karamar Dukku domin gudanar da bincike a kan alakar su da kuma rawar da suka taka a wannan aika-aika.