Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya mika godiyar sa ga miliyoyin ‘yan Nijeriya sakamakon fitar farin dango da su ka yi wajen kadawa masa kuri’a, wanda tunanin jam’iyyar ke nuna cewa ita ce za yi nasara.

Atiku ya bayyana haka ne bakin mai taimaka masa a kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Phrank Shaibu a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja.

Sanarwar ta kara da cewa, jam’iyyar Pdp na dakon sakamakon zaben da aka yi a daukacin na’urar tantance masu kada kuri’a 176,000 da aka yi amfani da su a zaben da ya gudana a fadin Nijeriya.

Atiku Abubakar ya ce, ‘yan Nijeriya su kara hakuri nan da dan lokaci kadan mafarkin su da suka dade suna jira zai tabbata.

Leave a Reply