Jam’iyyar adawa ta PDP, ta musanta rahoton cewa kwamitin kawo zaman lafiya a fagen siyasar kasar Najeriya NPC, ya sa ta janye kudurin zuwa kotu domin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabarairu.

Shugaban jam’iyyar Uche Secondus, ya ce ba shakka kwamitin samar da zaman lafiyar da ke karkashin tsohon shugaban kasa na mulkin soji Janar Abdusalam Abubakar, ya gana da dan takarar su Atiku Abubakar, amma babu maganar janye kudurin zuwa kotu, illa korafe-korafen su da suka gabatarwa kwamitin.

Secondus, ya jaddada bacin ran su kan abinda ya kira cin zarafin masu kada kuri’a yayin zaben na shugaban kasa, a jihohin da aka san jam’iyyar ta PDP na da dimbin magoya baya, da ya ce sun hada da Rivers, Akwa Ibom, Bayelsa da kuma Cross Rivers, inda matsalar ta fi kamari.

PDP ta kuma bayyana mamakin yadda aka yi, yawan masu kada kuri’ar da suka fito a jihohin Yobe, da Borno, yayin zaben na shugaban kasa, ya zarta na jihohin yankin kudu maso kudancin Najeriya, duk da cewa wadancan jihohin na fama da matsalolin tsaro.