Hukumar wayar da kan jama’a a Najeriya NOA, ta bukaci rage yawan jam’iyyun siyasar kasar, don saukakawa jama’a kada kuri’un su, da ma hukumar zaben kasar, wajen gudanar da aikin ta.

Bukatar hukumar ta NOA, ta zo ne bayan kammala zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a makon da ya gabata, wanda jam’iyyu 71 suka fafata.

Shugaban hukumar a Jihar Adamawa, Ahmad Sudi, ya shaidawa manema labarai cewa, an tafka hasarar kuri’u masu yawa a zaben na makon jiya, la’akari da cewa akwai dubban jama’a da suka gaza tantance alamar jam’iyyar da suka so zaba, saboda yawan alamun da ke kan takardar jefa kuri’a, da kuma kamannin su.

A cewar Sudi, zai iya yiwuwa wasu da suka zabi jam’iyyar PCP da ta zo ta uku a zaben shugaban kasa da yawan kuri’u dubu 110 da 196, sun dauka PDP ce ganin cewa ko a kan takardar jefa kuri’a sunayen su na kusa, hakan kuma zai iya haifar da dangwala musu yatsa bisa kuskure.

Zalika da dama daga cikin wasu da suka zabi ADC da ta zo ta 4 a zaben na shugaban kasa da kuri’u dubu 97, da 874, sun yi zaton jam’iyyar APC ce.

NOA ta kara da cewa yawan jam’iyyun siyasar ya kuma haifar da tsaiko wajen kammala kidayar kuri’u ko tattara sakamakon zabukan da suka gudana.