Kwamitin zartarwa na Jam’iyyar APC ya dakatar da gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, da takwaran sa na jihar Ogun Ibikunle Amosun, daga jam’iyyar.
Rahotanni sun nuna cewa, an yanke shawarar dakatar da gwamnonin biyu ne a taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar saboda ana zargin su da yi wa jam’iyyar ta APC zagon kasa.
Kwamitin ya yi zargin a lokacin da APC ta je yakin neman zabe Ibekunle Amosun. ya sa yara suka rika jifa, sannan yana ta gangamin neman a zabi dan takarar gwamnan wata jam’iyya ba APC ba, Inji Sakataren walwala na jam’iyyar ta APC na kasa Ibrahim Kabiru Masari.
Sai dai wani na hannun daman gwamna Amason Abdullahi Suleman, ya ce shi yana ganin babu hannun gwamnan a ciki, kuma shi gwamna yana tare da Baba Buhari.
Shi ma gwamnan jihar Imo Okorocha, an zarge shi ne da laifin yi wa jam’iyya zagon kasa, inda yake goyon bayan wani dan takarar gwamna da ba na APC ba.
Sai dai a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, Sakataren yada labaran gwamna Okorocha, Sam Uwuemeodo, ya zargi shugaban jam’iyyar ta APC, Adams Oshiomole da kokarin ruguza jam’iyyar ta APC.