Mai Magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya yi karin haske dangane da kalaman da shugaban kasa ya yi a kan cewa wa’adin mulkin sa na biyu zai kasance mai tsauri.

Garba Shehu, ya ce shugaba Buhari yana nufin shekaru hudu masu zuwa ba masu sauki bane saboda daga wadannan shekarun babu saura.

Ya ce a fahimtar sa Buhari, na nufin zai yi gwaninta ne wajen cika alkawuran da ya daukar wa ‘yan Najeriya.

Shugaba Buhari dai ya yi wadannan kalaman ne a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da ministocin sa a lokacin da suka kawo masa ziyara a fadar shugaban kasa domin taya shi murnar lashe zabe.

Wadannan kalamai na shugaban sun kasance kalamai masu harshen damo ga ‘yan Najeriya domin kuwa tuni jama’a da dama suka fara bayyana ra’ayoyin su a shafukan sada zumunta dangane da fahimtar su a kan kalaman.

Leave a Reply