Jami’ar Karatu daga Gida wato NOUN a takaice, za ta gudanar da bikin yaye dalibai akalla dubu 20 da 799.

A tarihin yaye dalibai a jami’a dai, wannan ne karo na farko da wata jami’a a fadin Afrika ta yamma za ta yaye dalibai masu yawa kamar haka.

Da ya ke tattaunawa da manema labarai, Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdalla Adamu, ya ce daga cikin wadanda za a yaye akwai dalibai 103 da su ka samu takardar shaidar kammala digiri mai daraja ta daya.

Wannan dai shi ne karo na takwas da jami’ar za ta yaye dalibai, wanda za a gudanar a ranar Asabar, 23 Ga Maris, a harabar helkwatar jami’ar da ke Abuja.

Farfesan ya ci gaba da cewa, jami’ar ta kara samun gagarumin tagomashi a ranar 7 Ga watan Disamba na shekara ta 2018, ranar da Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan Dokar da Aka Yi Wa Garambawul ta jami’ar.

Ya ce wannan garambawul da aka yi wa dokar zai ba dalibai damar tafiya aikin bautar kasa, kuma wadanda su ka karanci fannin shari’a za su rika samun damar wucewa Makarantar Koyon Aikin Shari’a da Lauya ta Kasa.

Leave a Reply