Karuwan da ke yawon-ta-zubar a birnin Umuahia na Jihar Abia sun shiga wasan buya, tun daga lokacin da gwamnatin jihar ta kaddamar da shirin korar karuwai daga titunan birnin tare da kulle gidajen karuwan da ke garin Umuahia.

Rahotanni na cewa, yanzu haka karuwai a birnin Umuahia su na zaman dar-dar ne.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Litinin da ta gabata ne, Gwamna Okezie Ikpeazu ya bada umarnin rufe duk gidajen karuwan da ke cikin birnin, musamman wadanda ke a kan Titunan Orlu, da Kaduna da na kan titin Arochukwu da sauran su.

Gwamna Ikpeazu, ya kuma bada umarnin gurfanar da masu gidajen da su ka ajiye karuwai su na zaman haya a ciki, ya na mai umartar a gurfanar da masu wuraren da su ka bari ana tu’ammali da kuma shan haramtattun kwayoyi a wuraren su.

Gwamnatin jihar, ta ce gidajen karuwai da matattarar masu sha da sayar da kwayoyi sun zama maboyar bata-gari da masu aikata miyagun laifuffuka a jihar.

Leave a Reply