Shugabar Kotun Daukaka Kara Zainab Bulkachuwa, ta hori alkalan da za su gudanar da shari’un da su ka danganci kararrakin zabe da cewa, su tabbatar sun kauce wa yanke hukuncin son rai, kuma kada su yi hukunci bisa tsoron wani bangare.

Bulkachuwa ta yi wannan gargadi ne, yayin da ta yi wata ganawaqr musamman da masu shari’ar a birnin Abuja.

Zainab Bulkacuwa, ta kuma hore su da su kasance su ke rike da kotun su kuma hukunci a hannun su ya ke, ba tare da wani ya karkatar da akalar su ko nuna bangaranci ko tsoron wani ba.

Ta ce duk wanda cikakkun shaidu su ka tabbatar da cewa shi ne ya yi nasara, to a ba shi nasarar sa a ba wanda ya fadi rashin nasarar sa.

A karshe ta ja hankalin su game da irin gagarumin aikin da ke gaban su, inda ta bukaci su tabbatar sun jajirce wa aiki tukuru, tare da nuna kwarewa wajen yanke hukkunci.