Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta ce za ta ba sanatoci da ‘yan majalisar wakilai shadar lashe zaben ranar 23 ga watan Fabrairu na shekara ta 2019.
Sai dai hukumar ta ce wadanda sunayen su su ka bayyana a shafin ta na Intanet ne kawai za ta ba shahadar.
Kawo yanzu dai, sanatoci 100 ne a cikin kujeru 109 da Nijeriya ta ke da su hukumar ta bayyana sunayen su, yayin da ta ce za ta sanya sunayen sanatocin da su ka lashe zaben da aka sake yi a ranar 9 ga watan Maris.Yanzu haka dai Sanatoci 100 da aka bayyana sunayen su, 62 ‘yan jam’iyyar APC ne, sai kuma 37 na jam’iyyar PDP da kuma guda daya na jam’iyyar YPP.