Gwamnan jihar Sokoto kuma dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP Aminu Waziri Tambuwal, ya ce ba su ga dokar da hukumar zabe ta dogara da ita wajen bayyana sakamakon zaben Sokoto a matsayin wanda bai kammala ba.

Tambuwal ya kira taron manema labarai, inda ya ce yayin da hukumar zabe ke bayyana rashin kammaluwar zabe da tanadin dokar zabe, sun dubi kundin tsarin mulki da tanadin dokar zabe ba su ga wannan tanadi ba.

Ya ce hukumar zaben ba ta bayyana masu runhunan zaben da aka soke zabubbukan su da kuma dalilan da su ka sa aka soke ba.

Tambuwal, ya ce akwai dalilan da ke sa a soke zabe ta yadda ba za a sake yi ba, akwai kuma dalilan da ke sa a soke amma a sake wani sabo.