Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kaddamar da kwamitin Shugaban kasa a kan cin gashin kan majalisun jihohi da bangaren shari’a na jiha kamar yadda ya ke kundin tsarin mulki.
Kwamitin mai dauke da mutane 16, ya hada da ministan shari’a Abubakar Malami a matsayin shugaba, yayin da mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin majalisar dattawa Sanata Ita Enang zai kasance sakataren kwamitin.
Yayin da ya ke kaddamar da kwamitin a fadar shugaban kasa da ke Abuja, shugaba Buhari ya bukaci ‘yan kwamitin su sanya kwazo wajen gudanar da aikin su.
Shugaban Buhari, ya ce kwamitin ya na lokaci na tsawon watanni uku domin kammala aikin sa, sannan ya bukaci ‘yan kwamitin su tabbatar da yin aiki a kan tsari.