Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta ce ta kammala shirin gudanar da zaben gwamna da za a sake a fadin kananan hukumomi 28 da ke jihar Kano.

Kwamishinan zabe na jihar Farfesa Riskuwa Arab-Shehu ya bayyana wa manema labarai haka a Kano, gabannin zaben da za a sake yi a ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

A cewar sa, a fadin kananan hukumomi 28, akwai cibiyoyin rijista 75, da mazabu 207 da kuma wuraren zabe 276 da yawan adadin masu rijista dubu 128 da 324.

Arab-Shehu, ya ce an soke zabe a fadin kananan hukumomi 15 ne saboda rikici, sannan mazabu 116 abin ya shafa, ya na mai cewa yankunan da abin ya shafa su na da masu zabe dubu 73 da 173.

Ya ce hukumar ta sake duba dukkan mazabun da abin ya shafa, sannan ta gano ainahin adadin kananan hukumomin da matsalar ta shafa. Kwamishinan, ya ba dukkan jam’iyyun siyasa tabbacin cewa, hukumar zabe za ta yi bakin kokarin ta don tabbatar da adalci da gaskiya a zaben da za a sake gudanarwa a jihar Kano