Babban Lauya kuma mai rajin kare hakkin dan adam Femi Falana, ya tuhumi ministan shari’a Abubakar Malami da aikata ba daidai ba a kan maida wasu ‘yan Kamaru kasar su.

Wannan dai, ya na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aike wa ministan ya kuma raba wa manema labarai.

A cewar lauyan, ‘yan gudan hijira masu neman mafaka ne, kuma dokoki da dama ciki har da kundin tsarin mulkin Nijeriya sun kare su daga muzgunawa daga hukuma a duk kasashe, don haka a Nijeriya bai kamata abin ya zama daban ba.

Lauyan ya cigaba da cewa, a matsayin sa na mai rajin kare hakkin dan Adam, ya dauki alkawarin kare ‘yan gudun hijirar kuma zai cigaba da bin kadin hakkokin su.

Leave a Reply