Jam’iyyar PDP ta na zargin hukumar zabe da hada baki da gwamnati da wasu manyan jami’an tsaro domin shirya magudi a zaben da za a sake yi a wasu jihohin Nijeriya.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan, ya ce tuni wasu manyan jami’an hukumar zabe sun gudanar da taro da takwarorin su na fadar shugaban kasa da jami’an tsaro domin shirya yadda za a kwace nasarar da ‘yan takarar jam’iyyar PDP za su yi a zaben da za a maimaita.

A nata bangaren, Hukumar zabe ta ce tabbas jami’an ta sun gana da manyan jami’an tsaron Nijeriya, amma wannan taro ne da ake yi lokaci zuwa lokaci domin tabbatar da tsaro a lokacin zabe.

Ologbondiyan, ya ce a duk jihohin da ya kamata a sake zaben, ‘yan takarar su ne ke sahun gaba.

Hukumar zabe dai ta yanke shawarar sake gudanar da zaben gwamnoni a jihohin da su ka hada da Adamawa, da Benue, da Sokoto, da Filato da Kano da kuma Bauchi, sakamakon kura-kuran da aka samu a zaben ranar 9 ga watan maris.