Bola Ahmed Tinubu, Jagoran Jam’iyyar APC
Bola Ahmed Tinubu, Jagoran Jam’iyyar APC

Jagoran Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya yi watsi da rade-radin da ke cewa ya ziyarci jihar Kano domin tsoma baki a zaben Gwamna da za a sake gudanarwa a wasu yankunan jihar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Tinubu ya ce bai ziyaci Kano ba tun bayan fara gudanar da zabubbukan da su ka gabata.

Ya ce hoton sa, tare da Gwamna Abdullahi Ganduje da ake yadawa, tun shekara ta 2018 su ka dauka, lokacin da Ganduje ya kai wata ziyara Lagos.

Tinubu ya ce, ire-iren wadannan rade-radin su na cutar da dimokradiyar da Najeriya ke fatan kafawa, kuma illa ce ga ci-gaban siyasar jihar Kano, ya na mai cewa shi cikakken mai son tsarin dimokaradiya ne, don haka ba zai aikata duk wani abu da zai gurgunta tsarin gudanar da zabe ba.