Mohammed Abubakar, Gwamnan Jihar Bauchi
Mohammed Abubakar, Gwamnan Jihar Bauchi

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta dage sauraren karar da Gwamna Mohammed Abubakar na Jihar Bauchi ya kai Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC.

Abubakar dai ya shigar da karar ne, ya na kalubalantar yadda hukumar ta sauya shawarar sake kidaya kuri’un Karamar Hukumar Tafawa Balewa, maimakon zaben da ta ce za ta sake a wuraren da ake tankiya.

Gwamnan ya kara da cewa, tunda har Babban Jami’in Zabe na Jihar Bauchi Mohammed Kyari ya sanar da cewa zabe bai kammalu ba, to hukumar zabe ba ta da hurumin da za ta ce zabe ya kammalu.

Mai shari’a Inyang Eko, dai ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 21 Ga Maris na shekara ta 2019.