Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara Celestine Okoye ya ce rundunar sa ta samu nasarar kama wata mota makare da kayayyakin zabe da za a ka su sokoto daga Abuja.

Okoye ya ce bincike ya nuna cewa, wasu ne da ba su da izinin daukar kayan zabe suka loda kayayyakin domin kai su jihar Sokoto.

Kwamishinan ya kara da cewa, rundunar ta kama motar da kuma  direban ta sannan ta na gudanar da bincike a kan lamarin.

Celestine Okoye ya kuma kara da cewa, jami’an tsaron su bas u yi kasa a gwiwa ba wajen ganin sun kama duk wadanda bai kamata ya mallaki wani abu na zabe ba, sannan sun dauki duk wani matakan da zai taimaka wajen ganin sun kare kayayyakin zaben da za a yi amfani da su a lokutan zabukan da za a gudanar a wannan shekara.