Muhammadu Buhari, Shugaba Kasa
Muhammadu Buhari, Shugaba Kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci masu kada kuri’a su fito su zabi dan takarar da suke so a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu domin cika hakkin da ya rataya a wuyan su a matsayin su na ‘yan kasa.

Buhari ya bayyana haka ne  a jawabin da ya gabatar  ga ‘yan Nijeriya  a ranar Juma’ar nan a Abuja, ya ce hakki ne da duk wanda ya isa zabe ya fita ya zabi gwamnatin da za ta jagoranci Nijeriya.

Shugaba Buhari ya kuma bayyana cewa, akwai bukatar yin wannan kira, domin zabe shine mafi girman ‘yanci da ‘yan kasa ke da shi ta yadda za su zabi gwamnatin da suke so ta wakilce su a dukkanin matakai, musamman wadda  za ta jajirce wajen tabbatar da jin dadin su da kuma kare hakkin su.

A karshe shugaban kasa Shugaban kasar ya kuma yi kira ga al’umma da kada su bari wani ya karya masu gwiwa ta hanyar hana su fitowa yin zabe a gobe Asabar.