Hukumar shiga da fice ta kasa ta bada umurnin kulle daukacin iyakokin Nijeriya da ke makwabtaka da sauran kasashe daga karfe 12 na yau Juma’a zuwa 12 na ranar lahadi.
Kakakin hukumar Sunday James ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a madadin shugaban hukumar Muhammad Babandede.
Ya ce gwamnatin tarayya ta bada umurnin kulle dukkanin iyakokin Nijeriya daga karfe 12 na ranar Juma’a zuwa karfe 12 na ranar Lahadi 24 ga watan Febrairun shekara ta 2019.
James ya kara da cewa, an dauki
wannan mataki ne domin hana shige da ficen kayayyaki a lokacin gudanar da zabe, saboda haka ake sanar da al’umma
cewa an kulle dukkanin iyakokin Nijeriya da su ka kunshi Nijar da Chadi, da kuma Kamaru.