Sabbin alkaluman kiwon lafiya na duniya sun nuna cewa, Nijeriya ce ta farko a jerin kasashen da su ke fama da cutar kyanda, inda alkaluma su ka nuna akalla sama da yara miliyan uku ne ba a yi masu riga-kafin cutar ba a halin yanzu.
Jami’in da ke kula da hukumar lafiya ta duniya a jihar Borno Dakta Audu Idawo ya bayya haka, yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar domin tunkarar aikin rigakafin cutar.
Ayyukan riga-kafin dai za su gudana ne daga a ranakun 21 zuwa 25 ga watan Maris, tare da hadin gwiwar ma’aikatar lafiya ta tarayya da asusun tallafa wa kananan yara na majalisar dinkin duniya.