Shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara, ya bayyana zaben shekara ta 2019 a matsayin abin dariya, ya na mai cewa duk wadanda su ka yi kokarin samun ,adafun iko ta kowane hali za su san makomar su.
Dogara ya bayyana haka ne, a wajen wani taron gaugawa da kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP ta kira a sakatariyar jam’iyyar na kasa da ke Abuja.
Yakubu Dogara, ya kuma kalubalanci hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC a kan yadda ta gudanar da zaben shekara ta 2019.
Shugaban majalisar ya cigaba da cewa, duk masu son kwace mulki ba don su taimaki mutane ba za su yi nadama.
A nasa bangaren, Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki, ya ce nasarar da jam’iyyar APC ke tutiyar ta samu a zabubbukan da aka kammala ta wucin-gadi ce.
Ya ce sakamakon zaben shugaban kasa tamkar asara ce ga kasa baki daya ba ba ma jam’iyyar PDP kawai ba.