Babbar kotun jihar Adamawa ta bada umarnin dakatar da gudanar da karashen zaben gwamna a jihar har sai abin da hali ya yi.

Rahotannin sun bayyana cewa, alkalin kotun Mai Shari’a Abdul’aziz Waziri, ya ce Hukumar Zabe ta dakatar da gudanar da zaben har sai an yanke hukunci a kan karar da dan takarar gwamna na Jam’iyyar MRDD ya shigar.

Jam’iyyar MRDD da dan takarar ta Eric Theman, sun bukaci kotu a soke zaben da aka gudanar a jihar makonni biyu da su ka gabata, inda su ka ce ba a buga tambarin jam’iyyar a kan takardar kada kuri’a ba. Sai dai babban lauyan hukumar zabe Tanimu Inuwa, ya roki kotun ta yi watsi da karar saboda a cewar sa ba ta da hurumin sauraren karar.