Kotun daukaka kara, ta umarci hukumar zabe ta mika wa Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP takardu da na’urorin da aka yi amfani da su a zaben shugaban kasa domin bin diddigin yadda aka yi zabe a Nijeriya.

Alkalin kotun Abdul Aboki, ya ce dokar Zabe ta yarda duk wanda ya ke da korafi a kan sakamakon zabe ko yadda aka gudanar da shi a ba shi damar bincikar takardun da kuma na’urorin da aka yi amfani da su.

Sai dai duk alkalai uku da su ka yi zaman yanke wannan hukuncin, sun ki amincewa da neman a yi binciken keke-da-keke ta yadda za a bi kowacce kuri’a da aka kada da ita kanta na’urar tantance masu kada kuri’a.

Kotun, ta ce ba za ta amince a mika wasu takardun da aka shigar da sakamakon zabe domin a yi bincike ba, kuma ba ta amince a mika wa Atiku na’urar da aka yi amfani da ita wajen shigar da sakamakon zabe domin yin binciken keke-da-keke ba.

Idan dai ba a manta ba, tun bayan da aka bayyana sakamakon zaben shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce bai yarda da sakamakon ba, domin domin an tafka magudi da murdiya shi ya sa bai yi nasara ba.