Shugabannin jam’iyyar APC na yankin Kudu maso Kudancin Nijeriya, sun bukaci a ba su mukamin shugaban majalisar dattawa.
Wannan bukata kuwa sun mika ta ne, a cikin sakon taya murna da su ka aike wa Shugaba Muhammadu Buhari a kan nasarar da ya samu ta lashe zaben shugban kasa da ya gabata.
A cikin sakon, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na yankin Ntufam Etta, ya ce yankin ya cancanci a ba shi wannan matsayi, domin ya dade ya na bada gudunmuwar ciyar da kasa gaba.
Ya ce shugabanin jam’iyyar sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin, domin ganin kasuwanci ya cigaba da kuma wayar da kan matasa game da muhimmancin zaman lafiya.