Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta bukaci gwamnatin tarayya ta fara biyan sabon ma fi karancin albashi ga dukkan ma’aikatan Nijeriya kafin nan da watan Mayu.
Mukaddashin shugaban kungiyar Najeem Yasin ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Nijeriya a Abuja.
Yasin ya kuma yaba wa majalisar dattawa a kan yadda ta amince da Karin mafi karancin albashin na naira 30,000.
Idan dai ba a mataba, kafin zabukan shekara ta 2019 majalisar wakilai ta amince da kudirin mayar da ma fi karancin albashi na naira dubu 30,000.
Da farko dai kungiyar gwamnoni ta fara yin tayin biyan naira dubu 24 a matsayin ma fi karancin albashi yayin da gwamnatin tarayya ta yi tayin naira dubu 27.
A karshe kungiyar NLC ta yaba wa majalisar dattawa bisa amincewar da ta yi na mafi karancin albashin naira dubu 30,000, sai dai har yanzu da sauran rina a kaba domin kuwa hankalin ma’aikata ba zai kwanta ba sai an fara biyan su sabon ma fi karancin albashin.