Gwamna jihar kano Abdullahi Ganduje ya ce gwamnatin sa ba za ta yarda da yunkuri da tada zaune tsaye ba daga kowace kungiya ko mutum a fadin jihar.
Ganduje ya yi gargadin ne a ranar Talatar da ta gabata a lokacin da kungiyoyin hadin gwiwa 320 na jakadun zaman lafiya suka kai masa ziyara.
Gwamna Ganduje ya kara da cewa, ba za su amince da tada zaune tsaye ba, sannan gwamnati ba za ta nade hannu tana kallon wasu mutane suna hargitsa jihar ba.
Kungiyar jakadun zaman lafiyar sun ba gwamna Ganduje tabbacin wanzar da zaman lafiya kafin lokaci da kuma bayan sa ke zaben da ba a kammla ba a jihar.