Dan takarar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar PDP a jihar Kaduna  Ashiru Kudan ya ba daukacin al’ummar  jihar tabbacin cewa za a kwato masu kuri’un su.

Kudan ya ce an yi wa mutanen jihar kaduna fashin kuri’u a zaben gwamna da aka gudanar a ranar asabar 9 ga wata Maris, sannan ya ce shi da jam’iyyar sa ta PDP sun kafa tawagar lauyoyi domin tabbatar da cewa an ba su hakkokin su.

Wasu kungiyoyi karkashin jagorancin Farfesa Banake Sambo sun lura cewa, ba a yi amfani da na’urar tantance kuri’u ba a wasu mazabun kananan hukumomi 10 a zaben jihar da hukumar INEC ta bayyana gwamna Nasir El-Rufai a matsayin wanda ya yi nasara.

Daga cikin kananan hukumomin da aka yi zargin ba a yi amfani da na’urar tatance masu kada kuri a ba sun hada da Giwa da Zaria da Sabon-Gari da Ikara da Lere da Igabi da Soba da kudancin Kaduna da kuma arewacin Kaduna.

Da yake mika sakon godiya ga mutanen jihar bayan an kammla zaben, Ashiru ya bayyana cewa zai bi hakkin kuri’un da su ke nasa a kotu, wanda a cewar sa an kwace masa ne ta hanyar amfani da karfin mulki.