Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar zartarwa ta kasa a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.
Hakan kuwa ya na zuwa ne, a daidai lokacin da ake rade-radin cewa shugaba Buhari ya tafi kasa mai tsaki domin yin aikin Umrah.
Rahotanni sun ce an fara zaman ne a lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya isa zauren taron da misalin karfe 10:59 na safe.
Daga cikin mahalarta taron kuwa akwai mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbaj, da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, da mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Babagana Munguno da kuma ministoci 23.
A baya dai an yada jita-jitar cewa, shugaba Buhari ya kama hanyar zuwa kasar Saudiyya domin gudanar aikin Umrah, kuma tuni ya mika ragamar kula da Nijeriya a hannun mataimakin sa Yemi Osinbajo.