Majalisar dattawa ta dage zaman ta zuwa nan da makonni biyu domin a ba Sanatoci damar maida hankali a kan lamuran da su ka shafi tattalin arziki.

Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa Ahmed Lawan ya gabatar da batun dage zaman majalisar, inda ya roki ‘yan majalisar su dage zaman su har zuwa ranar Talata, 2 ga watan Afrilu.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Talata, 19 ga watan Maris ne kasafin shekara ta 2019 ya shiga zagaye na biyu a majalisar dattawan, inda aka bukaci kwamitinta kasafi ya yi aiki a kan kasafin naira triliyan 8 da biliyan 8.

A wani bangare kuma, rahotanni sun bulla cewa, shugabannin jam’iyyar APC za su yanke hukunci a kan yadda za a raba mukaman majalisar dokoki ta kasa a mako mai zuwa.

Leave a Reply