Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare ta Afrika ta Yamma WAEC, ta bada sanarwar sakamakon jarabawar da dalibai su ka rubuta a cikin watan Janairun da ya gabata.

Wannan ne dai karo na biyu da aka kara samun gagarumar rashin nasara tun daga lokacin da aka fito da tsarin jarabawar a shekara ta 2018.

Isaac Adenipekun, Shugaban Hukumar  Shirya Jarabawar Kammala Sakandare Ta Afrika Ta Yamma WAEC
Isaac Adenipekun, Shugaban Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare Ta Afrika Ta Yamma WAEC

Yayin da ake bayyana sakamakon jarabar a Ofishin Hukumar na Kasa da ke Lagos, shugaban hukumar Isaac Adenipekun, ya ce dalibai dubu 12 da 202 ne su ka yi rajista, amma dubu 11 da 892 ne su ka rubuta jarabawar.

Adenipekun, ya ce mutane dubu 3 da 102 ne kadai su ka samu sakamakon sama da darussa biyar, wadanda su ka hada da Turanci da lissafi.

Ya kuma tunatar da cewa a shekarar da ta gabata, kashi 17 da rabi cikin 100 ne kacal su ka samu nasarar darussa biyar ko sama da haka.

Adenipekun, ya ce an rike sakamakon jarabawar dalibai sama da 300, saboda akwai zargin magudi ko satar jarabawa da ake yi masu.