Kotun daukaka kara da ke zama a Jalingo na jihar Taraba, ta yi watsi da hukuncin haramta wa dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC Alhaji Sani Abubakar Danladi takarar zabe.

Idan za a iya tunawa, a baya kun ji wata babbar kotun tarayya da ke Jalingo, ta janye dan takaran gwamnan jihar na jam’iyyar APC Sani Abubakar Danladi daga zaben ranar Asabar mai zuwa.

Kotun dai ta yanke hukuncin ne, bisa zargin karyar yawan shekarun da dan takarar ya yi a takardun da ya aika wa hukumar zabe ta kasa INEC.

Leave a Reply