
Ana ci gaba da aikin ceto jama’a a wajen da wani bene mai hawa uku ya rushe a garin Ibadan babban birnin jihar Oyo.
Lamarin ya faru ne kusan kwana hudu bayan wani ginin mai hawa uku shi ma ya ruguje a jihar Lagos, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 20.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe shida na yammacin ranar Juma’a a Unguwar Sogoye da ke Molete a Ibadan.
Zuwa yanzu dai ba a iya sanin yawan mutanen da hadarin ya rutsa da su ba.
Amma da farko mai magana da yawun gwamnatin jihar ta Oyo, Toye Arulogun, ya ce suna tafiyar da komai yadda ya kamata ba tare da wata matsala ba.
Gidan mai hawa uku wanda ake kan aikin ginin shi ya rufta ne inda ya jikkata mutane da dama wasu kuma buraguzai suka birne su.