Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce Kano ce cibiyar siyasar sa tun bayan da ya shiga harkar siyasa a shekara ta 2003.
Ya ce Kano ta dade ta na ba shi goyon baya ko a lokacin da bai yi nasara ba.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne, yayin da wata tawaga daga kudancin jihar Kano su ka kai masa ziyarar taya murna a Abuja.
Ya ce ba zai iya gode wa mutanen Kano a kan tsayawar da su ka yi tare da shi a lokaci dadi da wuya ba.
Buhari ya kuma gode wa Sanata Kabiru Gaya, inda ya ce kokarin sa a matsayin Shugaban kwamitin aiki na majalisar dattawa ya kawo ci-gaba a gwamnatin sa tsawon shekaru hudu da su ka gabata.