Shugaban hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hukumar zabe ta dauki matakan ganin zaben gwamnoni da majalisar dokoki na jiha da za a yi ranar 9 ga watan Maris ya gudana yadda ya kamata.
Mahmud Yakubu ya sanar da haka ne a helkwatar hukumar da ke Abuja, yayin wani zama da ya yi da jami’an hukumar zabe na jihohi.
Ya ce za a yi zaben gwamnoni da na majalisar dokoki ta jiha a jihohi 29 ne kawai, wanda ya hada da zaben shugabanin kananan hukumomi da kansiloli duk a wannan rana.
Farfesan ya cigaba da cewa, hukumar ta yi zaman ne, domin ganin yadda za ta kauce wa matsaloli a lokacin zabe ta hanyar kawar da matsalolin da aka yi fama da su a lokacin zaben shugaban kasa da na majalisun tarayya.
Yakubu
ya ce bayan sun kammala wannan zama, hukumar za ta sanar da matakan da su ka
dauka domin samun nasara a zabubbukan da ke tafe.