Akwai yiwuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ruguje majalisar ministocin sa gabanin rantsar da shi zuwa wa’adin mulki karo na biyu.

A cikin wata hirar kai tsaye da gidan Talabijin a Nijeriya ya yi da Femi Adesina, ya ce babu tabbacin shugaba Buhari zai cigaba da tafiya da wasu daga cikin tawagar da ya yi wa’adin farko da su.

Femi Adesina, ya ce kafin ranar 29 ga mayun da za a rantsar da shugaba Buhari a wa’adi na biyu, zai sallami illahirin ministocin da ya yi aiki da su tsawon shekaru 4.

Ya ce rusa majalisar ministocin ba sabon abu ne ba, domin haka doka ta tanada, kuma shi ne zai banbance gwamnatin farko da ta wannan karon.