Akalla sanatoci masu ci 64 da ‘yan majalisar wakilai 151 ne ba za su koma majalisar dokoki ta tarayya ba.

‘Yan majalisar dattawa 45 ne kawai da kimanin ‘yan majalisar wakilai 209 ne za su koma majalisar.

15 daga cikin sababbin sanatocin da aka zaba sun kasance tsoffin gwamnonin jiha, sannan 42 daga cikin sanatoci 64 da ba za su koma ba, sun rasa kujerun su ne tun a watan Oktoba na shekarar da ta gabata a zaben fidda gwani na jam’iyyun su.

Sauran ‘yan majalisa 22 kuma sun sha kaye ne a zaben majalisar dokoki da ya gudana a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu.

A majalisar wakilai kuwa, adadin ‘yan majalisar da ba za su koma ba ya kai kashi 41 na ‘yan majalisa 360, sai dai ana sa ran adadin zai karu, domin har yanzu ba a kaddamar da sakamakon wasu mazabu ba.