Jam’iyyar PDP a jihar Jigawa, ta ce mai yiwuwa ba za ta shiga zaben gwamnan jihar da za a yi ranar 9 ga watan Maris, matukar ba a cire Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bala Senchi daga jihar ba.
PDP ta yi zargin cewa an tabka magudi a zaben shugaban kasa, domin an sayi kuri’u kuma ‘yan sanda sun rika cin zarafin magoya bayan ta a jihar.
Dan takarar sanata Mustapha Lamido ya bayyana haka, a cikin wata hira da aka yi da shi a Gidan Radiyon Freedom da ke birnin Dutse na jihar Jigawa.
Mustapha ya fito takarar sanatan Jigawa, amma wanda ke kai Sabo Nakudu ya kada shi, sai dai ya yi zargin cewa an tafka magudi da kuma cin zarafin ‘yan adawa a fadin jihar.
Dangane da magudi kuwa, ya ce sau biyar ya na kiran kwamishinan ‘yan sanda ya na sanar da shi inda aka yi satar akwati, amma babu abin da aka yi.