Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa zata goyi bayan duk wani shiri na kasashe masu arzikin man Fetur OPEC na rage yawan man da zata hako saboda kyautata farashin sa a kasuwannin duniya.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne ta bakin babban mai bashi shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Malam Shehu Garba.

Garba Shehu ya ce shugaba Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da karamin ministan kula da al’amuran nahiyar Afrika kuma jakadan Sarki Salman bin Abdul’aziz Ahmad Qattan a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, Nijeriya kasa ce wacce ta ke mutunta kungiyar kasashe masu arzikin man Fetur ta OPEC, domin haka zata bada hadin kai a duk lokacin da ta bukaci a rage yawan man fetur da ake hakowa don kyautata farashin man a kasuwannin duniya.

Buhari ya kuma ce, Nijeriya ta na bukatar kudade saboda irin matsalolin da take fama da su da suka jibanci fadin kasa da rashin ci-gaba da kuma yawan al’umma.

A karshe shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa, za su tattauna da ministan man fetur na kasa domin daukar matakan da suka dace.