Jakadan kasar Ghana a Najeriya Rashid Bawa, ya jaddada bukatar da take akwai na kara inganta dagantakar dake tsakanin kasar sa da Najeriya.

Bawa ya bayyana hakan ne a lokacin bukin cikar kasar Ghana shekara 62 da samun ‘yan cin kai wanda ya gudana a Abuja.

Ya ce dangantakar dake tsakanin kasashen 2 na da matukar muhimmanci kuma suna taimakawa wajen ci gabansu ta bangarori da dama.

Bawa ya kara da cewa rashin samun daidaito a tsakanin kasashe na taimakawa wajen haifar da talauci, cin hanci da rashawa da kuma durkushewar kasashen.

Ya ce dangantakar dake tsakanin kasashen Nejeriya da Ghana, ya kara inganta bangarori da dama da suka hada da kasuwanci, zuba jari a cikin shekaru 3 da suka gabata.

Sannan ya yi alkawarin cewa kasashen za su ci gaba da inganta dangantakar dake tsakaninsu na ‘yan uwantaka, tare da yabawa gwamnati da ‘yan Najeriya kan yadda suka natsar da kuwunansu a zaben da ya gabata.

Leave a Reply