Kungiyar IS ta yi ikirarin cewa, ita ce ta kai wa rundunar sojin Nijeriya hari a arewa maso gabas.

Sai dai rundunar sojin Nijeriyar ta ce, dakarun hadin gwiwa sun fafata da mayakan kungiyar, kuma sun kashe ‘yan bindiga 33 tare da kwace makamai da motoci.

A cikin wata wata sanarwa da ta fitar, kungiyar IS ta ce dan-kunar-bakin-wake a cikin wata mota ne ya hari wani gungun sojoji a garin Arege kusa da tafkin Chadi.

Harin na kunar-bakin-wake dai ba a saba ganin kungiyar na kai irin sa ba, ganin ta fi amfani da bindigogi ko abubuwa masu fashewa wajen kai wa rundunar sojin Nijeriya hari.

Rundunar sojin Nijeriya, ta ce ta na ci-gaba da aiki da rundunonin kasa da na sama daga kasashen Kamaru da Nijar domin yaki da masu tada kayar baya.