Jami’ar Tattara Sakamakon Zaben Gwamna na Karamar Hukumar Tafawa Belewa a Jihar Bauchi Dominion Anosike, ta ce rayuwar ta na cikin hatsari, domin ana yi mata barazana da kisa a Jihar Bauchi.
Dominion ta yi ikirarin ne a cikin wata wasika da ta aike wa Hukumar Zabe, inda ta ke rokon a ba ta dama ta bayyana a gaban kwamitin bincike domin ta fadi gaskiyar abin da ya faru har aka soke sakamakon zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa.
Sai dai kuma ta yi rokon cewa, ta fi so a yi zaman kwamitin ne a Abuja ba a jihar Bauchi ba.
Ta ce ta na fuskantar Barazana cewa za a kashe ta matsawar aka gan ta ko a cikin Bauchi ko a kewayen Bauchi.
Dominion ta ce ita ta jagoranci zaben da aka gudanar a Karamar Hukumar Tafawa Balewa, don haka ta yi amanna cewa akwai bukatar ta zo na bada bayanin abin da ya faru har Kwamishinan Zabe na jihar Bauchi ya soke zaben. \�ֳ5�