Babbar asibitin tarayya da ke Jalingo, ta tabbatar da mutuwar mutane takwas da kuma jikkatar mutane 56 da ke jinya a asibitin sakamakon raunukan da su ka samu a rikicin zaben da ya faru a a farkon makon nan.

An dai sanya dokar ta-baci a birnin Jalingo tun ranar da aka sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar, wanda ya sabbaba rikici tsakanin ‘yan jam’iyyun hamayya, inda aka rasa rayuka tare da asarar dukiyoyi masu yawa.

Wata majiya ta ce mutane biyar sun mutu kafin a isa asibiti, yayin da sauran uku su ka cika a cikin asibitin.

Talatin da shida daga cikin mutanen kuma su na cikin halin mutu-kwakwai-rai-kwakwai, yayin da 47 ake kyautata zaton za su samu sauki ba da dadewa ba.