Abdullahi Umar Ganduje , Gwamna Jihar Kano
Abdullahi Umar Ganduje , Gwamna Jihar Kano

Daya daga cikin manyan Lauyoyin da ke neman gaskiya ta fito game da zargin da ke kan gwamna Abdullahi Umar Ganduje da karbar rashawa Audu Bulama Bukarti, ya yi shirin shiga kotu da hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC.

Babban Lauyan ya yi barazanar zuwa har gaban Alkali da hukumar EFCC, bisa zargin Ganduje da karbar daloli a matsayin rashawa.

Tun farko dai Lauyan ya ce, za su hadu kotu da hukumar EFCC, matukar aka ki ba shi sakamakon binciken da aka yi a kan bidiyon da ke nuna Ganduje ya na amsar rashawa daga hannun wasu ‘yan kwangila kwanakin baya.

Audu Bulama, ya tabbatar da cewa kusan ya kammala duk wani shirin da ake bukata na kai EFCC gaban Alkali, saboda rashin mika masa sakamakon binciken da ta yi game da sahihancin bidiyon Ganduje da aka saki a baya.

Ya ce ba zai bari zargin da ke kan gwamnan ya wuce haka nan ba tare da kotu ta dauki mataki ba.