Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, ya nesanta shugaba Muhammadu Buhari da kama-karyar da ya ce shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole ke yi.
Okorocha dai ya na maida martani ne a kan matakin da Oshiomhole ya dauka a karshen makon da ya gabata, na dakatar da shi da takwaran sa na jihar Ogun Ibikunle Amosun, bisa zargin su da yi wa jam’iyyar APC zagon kasa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun kakakin sa Sam Onwuemeodo, Okorocha ya zargi Oshiomhole da kokarin haddasa rikici tsakanin ‘yan jam’iyyar APC, inda ya ce ya na da tabbacin shugaba Buhari ba zai goyi bayan saba dokokin da shugaban jam’iyyar APC ke aikatawa ba.
Kalaman Rochas dai su na zuwa ne, bayan shugaban jam’iyyar APC na jihar Imo Daniel Nwafor ya bukaci Oshiomhole ya yi murabus, saboda kuskuren da ya ce ya tafka na dakatar da Rochas Okorocha da Ibikunle Amosun.
Yayin
wani taron manema labarai da ya kira, Nwafor ya ce matakin gaggauta dakatar da
gwamnonin ba tare da tabbatar da zargin yi wa jam’iyyar zagon kasa ba ya saba
ka’ida.